
Asalin hoton, Getty Images
Dan kwallon Manchester United Christian Eriksen ya ce a yadda yanayin kwallo yake tafiya, nan ba da jimawa ba za a iya mantawa da Cristiano Ronaldo a United.
A watan Nuwamba ne dan wasan Portugal din ya raba gari da United inda ya ce basa mutunta shi.
Eriksen ya ce ya ji takaicin tafiyar Ronaldo.
“Ina tunanin bayan wasanni biyu mutane za su iya fara mantawa da shi”.
Akwai rahotannin da ke nuna cewa Ronaldo zai iya koma wa kungiyar Al Nassr ta Saudiyya a kan Euro miliyan 200.
A halin yanzu, Manchester United ta samu nasara a wasanni biyu tun bayan kammala gasar cin kofin duniya, inda ta doke Burnley a gasar EFL sannan kuma ta lallasa Nottingham Forest da ci uku da nema a gasar Premier.
A ranar 31 ga watan Disamba United za ta ziyarci Wolves kuma tana sa ran samun nasara a wasanni biyar a jere a karon farko tun a watan Afrilun 2021.