Mutanen shida sun mutu, 14 kuma sun jikkata a hatsarin mota a Sokoto


Mutane shida sun mutu wasu 14 kuma suka  raunuka a wani hatsarin mota akan hanyar Sokoto zuwa Jega, a jihar Sokoto.

Mista Sani Hamzat, shugaban hukumar kiyaye haɗura ta ƙasa FRSC a jihar Sokoto yace hatsarin yafaru ne a ranar Laraba.

Dukkannin mutanen na cikin wata motar akori kura dake ɗauke dasu da kuma kaya yayin da motar ta kubuce ta fada rami.

Yace dukkanin mutanen da abin ya rutsa da su jami’an hukumar ta FRSC sun kwashe su zuwa Asibiti.

Haka kuma wani hatsarin da  wasu motoci biyu suka yi ya lakume ran mutum ɗaya akan hanyar Sokoto zuwa Gusau.

Shugaban hukumar ya alakanta hatsarin da gudun wuce sa’a da kuma tukin ganganci.

Hamzat ya shawarci direbobi da su rika tabbatarwa motocinsu, gilashi da kuma taya na cikin yanayi mai kyau kafin su hau kan titi.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like