Mutum ɗan shekara 30 ya gurfana gaban kotu kan yiwa wata mahaukaciya fyade


Wani mutum mara aikin yi ɗake da shekaru 30 ya gurfana a gaban Babbar Kotun  Majistire dake Gombe kan laifin yiwa wata mahaukaciya mai shekaru 40 fyade.

Dan sanda mai gabatar da ƙara Insifekta Bako Shekari ya fadawa kotun cewa mutumin da ake zargi, Mustafa Adamu, mazaunin unguwar Jakada dake cikin birnin Gombe, ya aikata laifin ranar 12 ga watan Disamba 2017 lokacin da shiga dakin matar wacce suke zaune unguwa daya  tare.

Insifekta Shekari ya fadawa kotun cewa bayan ya samu damar shiga dakin mutumin da ake zargi da aikata laifin yayi amfani da karfin tuwo wajen yin lalata da matar, wacce aka tabbatar tana da tabin hankali.

Amma kuma mai laifin yaki amincewa da tuhume-tuhumen da ake masa saboda haka dan sanda me gabatar da ƙara ya nemi a kara saka wata ranar domin samun damar kammala bincike.

Kotun dake ƙarƙashin mai shari’a Babayo Abba Usman ta daga shari’ar zuwa ranar 12 ga watan Janairu domin cigaba da sauraron karar  inda ya kuma yi umarni da a tasa ƙeyar wanda ake zargi zuwa gidan yari.

You may also like