Mutum 12 Sun Mutu A Fadan Kabilanci A TarabaTARABA, NIGERIA – SP Abdullhi Usman kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Taraba ya tabbatar mana da cewa ‘yan bangan da ake zargin sun ware kansu ne suka tafi yin wannan aikin ba tare da sanin hukumar ‘yan sandn Jihar ba.

Ya kara da cewa yanzu haka rundunar ‘yan sandar Jihar ta aika da dakaru domin kamo wadanda ake zargin.

Kuma tuni sun samu nasarar kamo wasu biyu daga cikin wadanda ake zargin da aikata wannan mummunar kisan.

Mode Muhammad mai anguwar Zudai shima ya tabbatar mana da cewa ‘yan bangan sun kashe mutane goma sha biyu nan take a gaban sa kuma suka ce sai sauran sun bar rugar gaba daya.

Malan shehu Aliyu mahaifin wani yaron da aka kashe, ya bukaci gwamnatin Jihar da na tarayyyar Najeriya da su musu adalci akan wannan irin kisan gilla akan su ba dare barana a Jihar Taraba.

‘Yan Banga Sun Kashe Mutane Sama Da 12 A Yankin Zudai, Karamar Hukumar Bali Na Jihar Taraba

‘Yan Banga Sun Kashe Mutane Sama Da 12 A Yankin Zudai, Karamar Hukumar Bali Na Jihar Taraba

Alhaji Adamu Zubai dagacen Zudai ya ce yanzu haka dai ‘yan bangan suna nan cikin daji, sai abin da Allah yayi kan kawo karshen mastalar rashin tsaron da ya addabi yakin nasu.

A nasu bangaren kungiyar Sullubawa dake Jihar atabakin Alhaji Ardo Kiri, Ardon Sullubawa mazaunan yankin Bali da Gossol a Jihar Taraba, shi bai dauki wadannan a matsayin ‘yan banga ba ya daukesu tamkar ‘yan ta’addan ne wadanda aka dauki hayarsu domin kwace iko a Jihar.

Saurari cikakken rahoto daga Lado Salisu Muhammad Garba:

You may also like