
Asalin hoton, EU in Nigeria/Twitter
Tawagar Ƙungiyar Tarayyar Turai da ta sa ido a zaɓen gwamnoni da na ƴan majalisar jihohi na ranar 18 ga watan Maris ta ce an kashe kimanin mutum 21 sakamakon tashin hankalin da aka samu a wasu jihohin Najeriya.
EU ta bayyana haka ne yayin da ake ci gaba da sanar da sakamakon zaɓen gwamnoni da na ƴan majalisar dokokin wasu jihohin.
Babban jami’in da ya sanya ido a zaɓen na Najeriya, Mista Barry Andrews ne ya bayyana wa ƴan jarida hakan ranar Litinin game da sakamakon bincikensu da suka yi game da zaɓen.
Barry ya ƙara da cewa mutane da dama ba su fita kaɗa ƙuri’a ba galibi a cewarsa saboda rashin biyan buƙatun masu zaɓe a zaɓen shugaban ƙasar da ya gudana.
Tawagar masu sa idon ta EU ta kuma ce an samu matsalolin da suka shafi sayen ƙuri’u a sassa daban-daban na ƙasar.
Ya kuma yaba wa hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya INEC saboda yadda ta gyara wasu kura-kuran da aka fuskanta a yayin zaɓen shugaban ƙasa musamman ta fuskar jigilar kayayyakin zaɓe.
Mista Barry ya kuma ce INEC ta inganta tsarin zaɓn ta hanyar aikewa da kuma amfani da na’urorin tantance masu zaɓe.
‘Matsalar sayen ƙuri’u ta mamaye zaɓen gwamnoni’
Ita ma Cibiyar Dimokradiyya da ci gaba ta Najeriya CDD ta ce matsalolin sayen ƙuri’u da kuma tashin hankali sun mamaye zaɓen gwamnoni da na ƴan majalisar dokokin jihohi na ranar Asabar.
Cikin wata sanarwa da shugaban Cibiyar nazari kan zaɓe ta CDD, Farfesa Adele Jinadu da Daraktar cibiyar, Idayat Hassan suka fitar, cibiyar ta ce hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC ta fi yin ƙoƙari ta ɓangaren jigilar kayan aiki abin da ya sa aka samu isar kayayyakin zuwa rumfunan zaɓe a kan lokaci.
CDD ta kuma koka kan matsalolin sayen ƙuri’u da tashin hankali da yi wa masu zaɓe barazana da aka samu a yayin zaɓen a wasu jihohi kamar Kano da Jigawa da Legas da Enugu da Bayelsa da Rivers da kuma Yobe.
Masu sa idon da cibiyar ta aike zuwa jihohin bakwai sun bayar da rahoton samun wuraren da wakilan jam’iyyu suka sayi ƙuri’u.