
Asalin hoton, ANI
Akalla mutum 35 ne suka mutu bayan faɗawa wata rijiya yayin da suke addu’a a wajen bauta da ke jihar Madhya Paradesh da ke tsakiyar India.
An ceto wasu mutum 14 na daban kuma har yanzu akwai wani mutum guda ɗaya da gani ba, a lamarin da ya faru a birnin Indore.
‘Yan sanda sun ce waɗanda abin ya rutsa da su suna tsaye ne kan wani kankaren siminti da ya rufe wagegen ramin, inda nauyinsu ya fi ƙarfinsa, sannan ya rufta.
Firaminista Narendra Modi ya ce “ ya kaɗu da wannan balahira da ta faru”.
Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis yayin da ake gudanar da bukin addu’a a wurin bauta na Beleshwar Mahadev Juhulelal ya shirya yayin bikin shekara na mabiya addinin Hindu na Ram Navami.
Gangamin masu bauta ne suka tsaya a saman kankaren da ya rufe rijiyar, inda nauyi ya yi masa yawa, abin da ya já mutane sama da 30 suka faɗa cikin rijiyar mai tsayin ƙafa 40.
Kafafen yaɗa labarai na jihar sun ce, an sake gina rijiyar ne bayan ginin da aka yi mata shekaru kimanin 40 da suka gabata.
Wani babban jami’i ya shaida wa gidan talabijin na ANI cewa an kai mutum 18 asibiti bayan an ceto su daga rijiyar, tuni kuma aka sallami mutum biyu daga cikinsu.
Ya ce har yanzu ana ci gaba da aikin bincike domin ceto waɗanda ba a gani ba.
Tawagar mutane 75 ciki har da na hukumar agajin gaggawa, su ne suke aikin ceton.
Mista Modi ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa yana miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda abin ya rutsa da su, sannan kuma za a bayar da kuɗi rupee 200,000 ga iyalan.