Mutum Daya Ya Rasa Ransa A Wajen Taron ‘Yan Kwankwasiyya A Jihar Kano


Rahotannin da suke fitowa daga garin Kura a jahar Kano na nuna yadda aka kashe wani matashi a gurin taron ‘yan Kwankwasiyya a bakin kasuwar Kura.

Rikicin ya samo asali ne yayin da aka zo ana raba jajayen huluna. Inda matashin suka fara sa-in-sa da wani, nan take ya daba masa wuka a ciki, inda aka dauke shi ranga-ranga zuwa asibitin Kura a nan rai ya yi halinsa. Inda jama’a suka farwa wanda yayi kisan da duka daga bisani suka mika shi ga jami’an tsaro.

You may also like