Wani wasan kwallon kafa wanda daga baya ya rikide ya zama rikici ya lakume ran magoyin bayan wata kungiya da aka bayyana da suna Obinna Chikwe, wasu mutane biyu kuma suka samu raumin harbin bindiga.
Lamarin yafaru ne a karamar hukumar Ikwo dake jihar Ebonyi lokacin wasan kwallon kafa tsakanin kungiyoyin da suka fito daga al’ummomin Ndufe Alike da Ndufu Echara dake buga wasan karshe na kofin da shugaban ƙaramar hukumar ya saka .
Jaridar Daily Trust ta gano cewa yan’sanda biyu suma sun jikkata a lamarin wanda wasan ƙarshe ne na gasar da ake kira “Gasar Kofin Haɗin Kai”.
Shedu sun ce rikicin yafara ne lokacin da alkalin wasa yabada katin rashin da’a ga ɗan wasan kungiyar Ndufu Alike wanda hakan ya jawo aka sakawa kungiyar kwallo ɗaya a raga da aka dawo hutun rabin lokaci.
Lamarin bai yiwa ɗan wasan daɗi ba inda ya yadawo cikin fili tare da sauran yan wasa dake zaune a benci suka farma alkalin wasan.
Lamarin ya harzuka matasan Ikwo wadanda suka kusa gwabza fada da jami’an yan’sanda.
Daya daga cikin masu fada aji yankin aya nuna rashin jin dadinsa kan yadda jami’an yan sanda suka yi amfani harsashin gaske wajen kwantar da tarzomar.