Mutum guda ya rasa ransa a wata arangama tsakanin yan shi’a da jami’an yan sanda a Abuja


An rawaito mutum guda ya rasa ransa lokacin da yan kungiyar yan uwa musulmi da aka fi sani da shi’a suka yi arangama da jami’an yan sanda a Abuja.

“An harbe shi har lahira lokacin da yake kokarin shiga lambun Unity Fountain tare da sauran yan uwansa ya yan kungiyar,” a cewar wani sheda da ya ganewa idonsa abinda ya faru.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne rundunar yan sanda ta bada sanarwar hana duk wata zanga zanga-a lambun amma yan shi’ar sun taru a wajen wurin inda aka hana su shiga ciki.

Masu zanga-zangar sun dage kan sai sun shiga ya yin da yan sanda suka ga abin na neman ya fi karfinsu sai suka fara harbin iska.

Wani harsashi da daya daga cikin jami’an tsaron ya harba ya fasa tagar wani ofishi dake hukumar sadarwa ta kasa NCC.

A yan kwanakin nan yan kungiyar ta shi’a na taruwa a lambun na Unity Fountain inda suke gudanar da zanga-zangar neman a saki jagoransu Ibrahim Elzakzaky wanda ke tsare a hannun jami’an tsaro.

You may also like