Mutum guda ya rasa ransa wasu da dama kuma sun jikkata a rikicin manoma da makiyaya a jihar Nassarawa


Mutum guda ya rasa ransa wasu da dama kuma suka jikkata a wani sabon rikici tsakanin manoma da Fulani a yankin Jankwe dake Karamar Hukumar Obi ta jihar Nassarawa. 
Wata majiyar dake yankin ta  shedawa jaridar Daily Trust cewa rikicin ya barke a kauyen  Duduguru sakamakon yinkurin da wasu Fulani suka yi na karɓo gatarin wani bafulatani wanda ya lalata kayan amfanin gona inda aka kwace gatarin nasa a matsayin sheda.

A cewar majiyar yinkurin karbo gatarin ya gamu da turjiya daga makiyayan a yammacin ranar Asabar inda abin ya rikide zuwa rikici da har ta kai da mutuwar  mutum guda da kuma jikkata wasu da dama.

Mai magana  da yawun rundunar yan’sanda ta  jihar Nassarawa,DSP Idrisu Kennedy ya ce rundunar ta samu labarin mutuwar mutum guda kuma tuni ta ƙara tura yan’sanda zuwa yankin domin shawo kan lamarin.

You may also like