Mutum na buƘatar taimakon Allah wajen yaƘi da cin hanci-Obasanjo


olusegun-obasanjo-600x400.jpg

Toshon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo yace mutum ba zai iya maganin cin hanci ba, batare da taimakon Allah ba.
Da yake jawabi a taron majami’ar Life Bible Church International dake jihar Ogun ,Obasanjo yace wa’azin da ake na cewa mutum zai iya samun dukiya batare da yayi aiki tuƙuru ba tamkar kiran mutane ne su aikata cin hanci.
Obasanjo ya samu wakilcin Femi Olajide shugaban majami’ar Glorious King church dake dakin karatun tsohon shugaban ƙasar.
Yayi nuni da rashin tarbiya a matsayin wata matsala da take damun al’umma.Obasanjo yace dole ne majami’o’i suyi amfani da matsayinsu wajen cusawa mutane kyawawan dabi’u.
“Mun ga yadda aka kawo cin hanci cikin duniyar da Allah ya samar.Mutum shi kadai da kansa bazai iya kawar da cin hanci ba daga doron ƙasa dole yana buƙatar taimakon Allah”yace
Coci suna bada gudummawa wajen cin hanci ta hanyar karɓar kyauta daga hannun mutane batare da tambayar inda suka samo ba.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like