
Asalin hoton, JO HOLLIS/BBC
Wani mutum a kudancin ƙasar Senegal ya ɗora wa kansa wani gagarumin aiki na dasa bishiya miliyan biyar nan da shekara biyar a cikin ƙasar.
Wannan aiki mai cike da tsinkaye ya zo wa Adama Dieme ne lokacin da ya koma gida yankin Casamance cikin shekara ta 2020, bayan ya shafe shekaru ƙalilan yana aiki a nahiyar Turai.
Mutumin mai shekara 48 ya gigice ganin a ƙauyukansu da ke da ɗaruruwan manya-manyan bishiyoyi lokacin ƙuruciyarsa, amma yanzu kaɗan ne suka rage idan ma akwai.
“A wasu ƙauyukan, ba kwa iya samun ko bishiya ɗay. Sun cire su, ba tare da sun yi tunanin sake dasawa ba,” ya faɗa wa BBC.
A faɗin Afirka, sare dazuka na ɗaya daga cikin dalilan da ake ɗora wa alhakin kwararowar hamada, amma a wannan yanki, har ma da faɗin makeken sashen Kogin Casamance, an fi samun yiwuwar sare bishiyoyi don yin gine-gine ko samun gawayi.
Mista Diémé, wanda yanzu yake aiki da wata ƙungiya mai zaman kanta a matsayin manajan aikace-aikace a Casamance, kuma mai aikin sa-kai a matsayin jami’in ba da horo kan harkokin noma, ya ƙuduri niyyar canza abubuwan da ke faruwa.
Ba tare da wasu maƙudan kuɗi ba, Adama Dieme ya fara neman gudunmawa don ganin mafarkinsa ya zama gaskiya – kuma ya fara amfani da ɗan abin da ke aljihunsa kimanin $5,000 don fara wannan yunƙuri.
Bijiro da ƙarfin halin mata
Yana aiki tuƙuru don ganin ya shigar da al’ummomin ƙauyukan a faɗin yankin kuma yana tuntuɓar mata, waɗanda ya san za su iya tunkarar ƙalubalen haɗa gangamin dasa bishiyoyi masu yawa.
Asalin hoton, JO HOLLIS/BBC
Matan da ke dasa bishiyoyin na iya girbar kayan marmarin da suke samu su sayar
“Idan ka je gari kuma ka ga babu mace, to bala’i ne ya auku,” in ji Adama Diémé.
“Amma idan ka je gari, ka ga mata ne kawai, to aljanna ce – suna da aiki tuƙuru kuma suna aiki ba dare ba rana.”
Abin da yake yi, shi ne haɗa wannan niyya tasa ta dasa bishiyoyi, da taimaka wa mata wajen samun ƙwarewar da za su iya zama ƙananan manoma kuma su sayar da amfanin gonakinsu a kasuwannin ƙauye.
“Da farko, ba mu san yadda za mu iya shuka iri, ko kuma yadda za mu yi shuka ba ma,” wata mata mai suna Safi Yetou, ta ce. “Amma yanzu muna da duk nau’o’in kayan marmari da muke sayarwa a kasuwa, kuma ba mu dogara da kowa ba. Mun buɗe asusun ajiya a banki yanzu, don haka babu wanda zai ce min yi kaza ko kada ki yi kaza. Wannan wani abin burgewa ne.”
Asalin hoton, JO HOLLIS/BBC
Adama Diémé (tsakiya), ana iya ganin sa a nan da irin tsamiya, yana cewa kowanne ƙauye su suke cewa ga irin bishiyoyin da suke so a dasa musu
Sunan aikin Adama Diémé Ununukolaal, wanda a harshen yankinsu na Jola ke nufin “Bishiyoyinmu”.
Nau’o’in bishiyoyi fiye da 12 ne ake dasawa, kama daga kwakwa da tsamiya da bishiyar rimi da lemon tsami – irin bishiyar, ya danganta da buƙatun ƙauyen, da kuma yanayin ƙasar da ke akwai.
A cikin sama da shekara uku, an raini iri fiye da 142,000 kuma tuni sun tasa.
Hakan na nufin sai Adama Dieme ya yi dashen bishiyoyi masu yawan ban mamaki kafin ya iya cika burinsa nan da shekara biyar – amma shi da abokiyar zamansa Yolanda Pereñiguez ba su karaya ba.
Misis Pereñiguez na aiki ne a matsayin tela kuma tana ba shi gagarumin taimako wajen tara masa gudunmawa ta hanyar ɗinka rigunan da akasari ake sayarwa a ƙasashen waje kan $15.
Ita da abokiyar aikinta Raymonde Coly, suna aiki a wani ɗan ƙaramin shago da kekunan ɗinki guda biyu, inda suke ɗinka rigunan da yadin da ake samu a cikin gida, kuma sai su buga tambarin wata babbar bishiyar kuka a gaban rigar.
Duk riga ɗaya da suka sayar, tana iya sayen irin bishiya 15.
“Na zaɓi bishiyar kuka ne a matsayin alama ko tambarin gaban rigar saboda ita ce bishiyar Afirka,” a cewar Misis Periniguiz.
“Abin burgewa ne sanin cewa waɗannan riguna suna shiga ko’ina a duniya, har Turai da Kanada don taimaka wa wannan aiki na dasa bishiya.”
Bishiyoyin Kuka za su ceci gidaje
Yayin da muka ƙara nutsawa cikin Casamance da ƙaramin kwale-kwale, wanda shi ma aka yi da shi da itacen rimi, haƙiƙanin darajar aikin dashen bishiyoyin na ƙara fitowa fili. A wani ƙaramin ƙauyen tsibiri da ke tsakiyar kogi, ruwa ya ci iyakoki har gaban gidaje – a wasu wuraren ma, ya shiga ƙarƙashi ya kwanta a ƙasan ginshiƙan da aka ɗora gidajen.
Asalin hoton, Jo HOLLIS/ BBC
Ruwa yanzu yana kwanciya a ƙarƙashin gidaje a wannan tsibiri da ke Kogin Casamance
Shekara goma da ta wuce, yawan ruwan gaɓar kogi na can nesa kuma da ƙyar yake iya kai wa cikin ƙauyen, sai dai fa a lokacin damuna marka-marka.
Yanzu lamarin ya gigita mutane, kuma ya munana, hakan na nufin mazauna ƙauyen za su kasance ba tare da matsugunnai ba.
“Muna rayuwa a wannan tsauni tsawon ɗaruruwan shekaru – amma idan ruwa ya ci gaba da ƙaruwa, sai dai mu bar nan mu warwatsu zuwa wasu yankuna,” a cewar Conakry Bassene, ɗaya daga cikin shugabannin ƙauyen.
Bishiyoyin kuka waɗanda za su iya rayuwa a kan tsandauri da kuma a kusa da ruwan teku ko na kogi, yanzu ana shuka su a gefen gaɓar kogi don su zama shamaki.
“Da ƙananan bishiyoyin nan masu kaɗawa cikin iska, da kuma alƙawarin ƙwazo wata ran su ba mu ‘ya’yan itace, wata ran su ba mu inuwa. Bishiyoyin nan za su iya kuɓutar da mu,” a cewar Conakry Bassene.”Bishiyoyin, su ne fatan na rayuwa a nan.”