N-Power: An Yi Kira Ga Masu Amfanuwa Da Su Zabi Na’uraA cikin wata takarda da mai taimaka wa gwamnan Bauchi na musamman akan sadarwa, Shamsuddeen Abubakar ya fitar a yammacin Laraba, yayi kira ga wandanda suke amfana da Npower da su gaggauta zabar na’ura.
Zabar na’urar dai zai kasance a yanar gizo ne inda za’a shiga sannan a bi matakai kamar haka:
1. Ka shiga kan profile naka a npvn.npower.gov.ng 
2. Ka dubi na’urori guda tara (9) da aka gabatar da su
3. Sai ka zabi na’ura guda da ta  dace da ayyukan ka.
To sai dai wannan tsari na sauya na’ura za’a yi shi ne cikin sati daya.
Haka kuma zaben na’uran shine na karshe kuma ba za’a sauya  ba matukar an zaba. Saboda haka ne ake shawartar mutane da su tabbatar sun zabi na’ura da ya dace da su.
Zaben na’uran wajibi ne saboda koyo da kuma aiki a karkashin shirin Npower. Kudaden na’uran sun banbanta, amma gwamnati zata saukar da kudaden kasa. Galibi ma daga cikin na’urorin kyauta ne, kadan ne suke sama da kudin gwamnati wanda hakan yasa masu amfanuwa zasu biya kudi da bai taka kara ya karya ba daga albashin su na Npower har na tsawon watanni 20. A saboda haka ne ma ake shawartar mutane da su dubi bayanan kudi kafin su zaba.

You may also like