Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce Ibrahim Magu, zai cigaba da zama kan kujerarsa ta shugabancin hukumar EFCC.
“Ba zan dakatar da shi ba saboda ban ga laifin da ya yi ba, kuma ina tabbatarwa da ‘yan Nijeriya, cewa ko akwai Magu ko babu shi zan yi yaki da cin hanci da rashawa saboda haka su kwantar da hankalinsu.