Na Cancanta na Zama Shugaba Kasa –  Sen. Ali modu sheriff


Tsohon gwamnan jihar Borno wanda kuma yanzu sanata ne a Jihar bornon,  wanda kuma ikirarin shima Shugaban jam’iyyar PDP ne na Kasa baki daya,  yace a matsayin shi na dan Nigeria ya Cancanta da Jam’iyyar tasa ta PDP data tsayar dashi takarar Shugaban kasa a gangamin jam’iyyar da za’ayi Ranar Labara 17/08/2016.

Sen. Modu sheriff ya kara da cewa duk da cewa ban gayawa kowa kudurina na cewa ina son zama Shugaban Kasar ba,  amma ina mai tabbatar wa da mutanen Najeriya cewa na Cancanta da na zama shugaban kasa kuma ina da duk wata nagarta ta zama Shugaban kasar.

Ya kara da cewa,  gaskiyar lamarin shine ban taba gayawa kowa cewar ina son zama Shugaban kasa ba.

You may also like