Na cika wa Al Nassr alkawari, duk da zawarcina da aka rika yi- Ronaldo



Ronaldo

Asalin hoton, Reuters

Kyaftin din Portugal Cristiano Ronaldo ya ce ya samu damammakin zuwa wasu manyan kungiyoyi kafin ya yanke shawarar zuwa Al Nassr.

A ranar Juma’a ne Ronaldo ya rattaba hannu da kungiyar ta Saudiyya, bayan yin baram-baram da tsohuwar kungiyarsa Manchester United.

Mai shekaru 37 din ya ce ya samu tayin zuwa kungiyoyi a Brazil, da Australiya, da Amurka da kuma kasarsa Portugal.

Sai dai a hirarsa ta farko da manema labarai yayin gabatar da shi ga magoya baya a Riyard, Ronaldo ya ce ”Na gama aikina a Turai.”



Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like