Na Dakatar Da jami’an Tsaro Wajen kama Fasto Suleiman –  Fayose



Gwamnan Jihar Ekiti kuma shugaban gwamnonin PDP, Ayodele Fayose yace ya dakatar da jami’an tsaron farin kaya (DSS) daga kama Fasto Johson Suleiman a garin Ado ikiti da asubahin yau Laraba.
Shi dai Jhonson Suleiman ya kasance taken labarai ne bayan ya yi wata magana akan rikicin Kaduna tsakanin makiyaya da ‘yan garin. Suleiman ya umurci mabiyan shi da su kashe Fulani a duk inda suka ganshi su kawo mishi kan gawar zai yi amfani da shi a matsayin baiko.
Suleiman yaje Ado Ekiti saboda wani taron kwana biyu wanda ya samu halartar gwamna Fayose, an bi bayan shi bayan ya kai ziyara ga gwamnan inda aka zagaye dakin hotel din da yake ciki, kaman yanda gwamnan Ekiti ya bayyana.
Fasto Suleiman nan take yace sai ya kira Fayose saboda ya sanar da shi abunda ke faruwa.
“Na zo Ado Ekiti saboda taro. Amma ina da sanin cewa ana bibiya ta bayan na nemi Kirista su kashe makiyaya fulani. Makiyayan sun mayar da yaran Kiristoci marayu da dama amma nace lokaci yayi da zamu kare kan mu,” inji fasto suleiman.
Shi kuma gwamna Fayose cewa yayi idan har jami’an tsaron farin kaya na son ta kama shi to kamata yayi ta gayyace shi tunda an san yana nan ba gudu zai yi ba.
“Ni da kaina na halarci taron shi kuma ina gani kuskure ne mutumin da bai da makami kuma za’a iya gayyatan shi a zo kama shi. Shin musulmai na da banbanci da Kiristoci ne a doka?” Inji gwamna fayose

You may also like