Na kashe yarinya na kuma sayar da sassan jikinta ₦8500 – Wani mutum da ake zargi da kisan kai


Wani mutum dan shekara 35 da ake zargin matsafi ne mai suna Yewunu Tanloju, ya bayyana yadda ya ja hankalin wata yarinya,Taye Gusinu, mai  shekaru 17 da ke sayar da abinci inda ya kashe ta bayan da ya sayi abincin ta na ₦40.

Tanloju na tare da wasu mutane 13 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban wanda kwamishinan yan’sanda na jihar Ogun,Ahmad Iliyasu ya gabatar da su ga manema labarai a hedikwatar rundunar dake Abeokuta.

Mai laifin ya kara da cewa ya daure hannun yarinyar kafin daga bisani ya yi mata yankar rago.

Mutumin da ake zargi tare da hadin kan wasu mutane biyu, Olusoji Asamo, mai shekaru 27 dake bada maganin gargajiya da kuma Joyi Isuru an kama sune a garin Arigo Ijopun dake karamar hukumar Ipokia.

Tanloju ya ce ya cire wasu sassan jikin yarinyar masu muhimmanci da suka hada da kanta, gabanta,al’urarta, zuciya hannaye biyu da kuma hanji inda ya jefa ragowar sassan jikin cikin rijiya.

Ya fadawa yan jarida cewa Asamo wanda shine ya bashi kwangilar samo sassan jikin ya bashi kudi ₦8500 ya kuma kara da cewa  wannan ne karo na biyu da yake kaiwa Asamo sassan jikin dan’adam.

Sauran masu laifin an kama sune kan aikata laifuka daban-daban kama daga sojan gona, fashi da makami, fyade da kuma shiga kungiyoyin asiri.

You may also like