
Asalin hoton, OTHER
Dan wasan gaban Faransa Karim Benzema ya rubuta a shafinsa na Tuwita cewa ya kawo karshen buga wa Faransa wasa.
Benzema wanda ya cika shekara 35 ranar Litinin, bai samu buga gasar kofin duniya ba saboda rauni, kuma kasarsa ta yi rashin nasara a wasan karshe 4-2 a bugun fenareti hannun Argentina.
Ya buga wa Faransa wasanni 97 kuma ya ci kwallaye 37.
Dan wasan wanda ya lashe kambun dan wasan duniya a yanzu ya bulguta cewa zai yi ritaya daga buga wa kasarsa wasanni.
Dan wasan gaban na Real Madrid bai buga wa Faransa wasa ba kusan shekaru shida, bayan badakalar da ya samu kansa shida tsohon abokin wasansa Mathieu Valbuena.
To amma an warware matsalar kuma ya dawo buga wa Faransa kwallo a gasar Yuro 2020.
Bajintar da Benzema ya nuna ta taimaka wa Real Madrid ta lashe kofin gasar zakarun Turai na 14 a tarihi, wanda hakan ya kai shi ga lashe kyautar dan kwallo mafi hazaka ta Ballon d’Or a watannin da suka gabata.