An Nada Sabon Kwamandan Sojin Rundunar Fada Da Boko Haram A Nijeriya


4bhf1e7c895005mwy_800C450 (1)

 

Rundunar sojin Nijeriya ta sanar da yin wasu sauye-sauyen wajajen aiki ga wasu manyan kwamandojinta ciki kuwa har da kwamandan Rundunar Zaman Lafiya Dole mai yaki da Boko Haram, inda aka nada wa rundunar sabon kwamanda wanda zai maye gurbin Manjo Janar Lucky Irabor.

Rahotanni daga Nijeriyan sun bayyana cewar kakakin rundunar sojin Nijeriyan, Birgediya Janar Sani Usman Kukasheka ne ya sanar da wadannan sauye-sauyen da aka yi a wata sanarwa da ya fitar inda ya ce a halin yanzu an nada Manjo Janar I. Attahiru a matsayin sabon kwamandan rundunar Zaman Lafiya Dolen wanda zai maye gurbin Manjo Janar Lucky Irabor wanda aka nada a matsayin kwamandan dakarun hadin gwiwa na kasashe daban-daban da ke fada da Boko Haram din.

Ita dai wannan runduna ta Zaman Lafiya Dole an kafa ta da kuma ba ta wannan suna ne a kokarin da ake yi na ganin bayan ‘yan kungiyar ta Boko Haram wanda ya zuwa yanzu ta sami nasarori masu yawa ciki kuwa har da kwato babbar helkwatar kungiyar ta Boko Haram da ke dajin Sambisa, bugu da kari kan karya lagon ‘yan kungiyar.

 

Har ila yau sanarwar ta yi sanar da sunayen wasu kwamandojin da manyan jami’an sojin da sauye-sauyen ta shafe su wadanda mafiya yawansu manya-manyan kwamandoji ne masu mukamai na manjo janar-janar.

You may also like