Nahiyar Afrika Na Iya Wargajewa Nan Bada Dadewa Ba – Obasanjo Obasanjo ya ce rashin adana kudin da gwamnatinsa ta bari na cikin abun da ya sa kasar ta shiga cikin halin karayar arzikin da ta fada. 
Olusegun Obasanjo ya shugabanci Nijeriya daga 1999 zuwa 2007 kuma yana da abubuwa da dama da zai fada kan lamarin da ya shafi kasar da kuma ke damun Afirka. A cikin hirarsu da wakiliyar BBC, lerato Mbele, ya fara ne da yin tsokaci game da tattalin arzikin Nijeriya.

Yanayin tattalin arzikin da muke ciki a kasar mu, ya tabarbare,ba wai don haka lamarin ya ke ba ako ina cikin duniya. Idan a shekarar 2007 da nake barin gwamnati kudin Najeriya a asusun tsimi sun tashi daga dalla bilyan 3 da digo 7 da na tarar a shekarar 1999 zuwa dala biliyan sama da 45, mun samu ci gaba daga rashin kudin rarar danyen mai, wannan rara ce tsakanin fdarashin da muka yi lissafin za mu sayar da mai a kasafin kudi da kuma farashin da muka sayar da mai.Sai muka ajiye kudin a gefe daya.Muka kuma bar sama da dalla bilyan 22 kan wannan.

Dukkan wadannan kudi da muka ajiye mun ajiye su ne domin su taimaka mana a lokacin kangi, sai gashi an yin amfani da su !!!An yi amfani da su ba tare da wani abun azo agani ba. .To ranar kangi ta zo bamu da abun kariya -ruwan sama na faduwa ba mu da lema domin mun yage lemar tamu. Sai abubuwa suka zo mana da ba zata.

To ka ce Nijeriya ba ta rike komai ba, saboda yadda mulki ya kasa ko kuma saboda cin hanci da rashawa?
Duka biyu! duka biyu!! Ma’aikatunmu na da rauni. Babu mulki na gari kuma muna da rashin jagorenci mai nagarta wanda ya hada da cin hanci. Su ne suka kawo hakan.
To idan muka dubi yadda Afirka take a yau, ko ka na alfahari da yanayin da nahiyar take ciki yanzu?
Kwarai ina Alfahari da zama dan Afirka saboda ba zan zabi kasancewa ba dan wani wuri can na daban ba.Mun samu ci gaba sai dai bai isa ba. Ba mu tafiyar da tattalin arzikin mu yadda ya kamata ba.Ba mu tafiyar da mulki ba yadda ya kamata ba. Mun dan kamanta game da zaben demokaradiya saboda shekaru 30 da suka gabata yin zabe a Afirka ya zama wani abu sabo. A yau yin zabe bai zama sabo ba.

Idan za ka wa yi magana ga shugabanin Afirka, masu shekaru da kuma wadanda suke mulki yanzu, me za ka rokesu da su yi tunani a kai me za ka ce su sa a gabansu?
A yanzu mutane na tambayata menene babban fargaba da nike da shi game da Afirka kuma ina cewa: matasa. Maganar illimi ta shafe kusan komai , aiki yi, mutuwar yara kanana,mutuwar mata wajen haifuwa, cututuka ko mai da ko mai. A lokacin da muke da sama da kashi 60 cikin dari na al’ummar mu ‘yan kasa da shekaru 25 ne kuma sama da kashi 50 cikin dari na wadannan al’umma basu da aikin yi, wannan abu mai hadari ne, kuma dukan mu muna zaune cikin wani yanayi mai hatsari da kan iya tarwatsewa a ko da yaushe.

You may also like