An daura auren Alhaji Yau Gimba kumo (Tsohon M.D na Federal Mortgage Bank) da amaryar sa Hajiya Fatima Muhammadu Buhari ‘ýa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a gidan sa dake garin Daura jihar katsina bisa sadaki #100,000
Wadanda suka sheda addu’ar auren sun hada da Ministan tsaro, Ministan harkokin cikin gida, Ministan albarkatun kasa, Sen.Danjuma Goje, Sen. Yariman Bakura, Gwamnan Bauchi, Gwamnan Gombe, Direkta SSS, AGF, Sarkin Daura da dai sauran jama’a da dama.
Bappan ango shi ya karba wa ango auren anyi addu’a Allah ya basu zama lafiya, da dukkan sauran angwaye Amiin.