Najeriya: 2016 tsaro da tattalin arziki sun cika zukata


 

A fanin siyasa kuwa rigingimun da ke faruwa a jamiyyar adawa ta PDP baya ga darewa gida biyu da ma kama hanyar rushewa, yayin da ita kanta APC ta ke zaki irin na ganga da ake tsoro me zai biyo baya.

Paris Medef Zentrale Buhari Gattaz (Getty Images/AFP/E. Piermont)

Shekara ta 2016 da ke shirin karewa ta kasance wacce ke cike da abubuwa da suka faru a Najeriya  musamman a fanonin tsaro, tattalin arziki siyasa da ma yaki da cin hanci da rashawa. To an bude shekarar ta 2016 a Najeriya ne da batun cin hanci da rashawa  musamman mumunar satar da aka bankado an tafka a fanin sayen makamai da bayan bincike aka gano an wawashe sama da Dala bilyan 15 ba ma wai bilyan 12 da ake tunanin ba. Mika rahoton binciken da aka gudanar ga shugaban kasa ya biyo bayan kame-kame da ma kwato kudade masu dinbin yawa daga hannun jama’a.

Batun kai samame  tare da kame wasu manyan alkalan da ake zargi da cin hanci da rashawa da shi ne irinsa na farko a tarihin Najeriya ya kasance wanda ya tada kura a 2016 mai karewa kamar yadda Dakta Abubakar Umar Kari masani a fanin kimiyar siyasa ya bayyana:

Nigeria Gerichtshof in Abuja (DW/U. Musa)

“A karon farko a tarihin Najeriya an ga jami’an tsaro sun fantsama a gidajen alkalai inda aka cafke wadanda ake zargi da cin hanci, a gidajen wasunsu an samu makudan kudade, wannan ya tada kura”.

Batun tsaro  kama daga yaki da ta’adanci ya zuwa na Fulani makiyaya musamman a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya da yawaitar sacewa ko garkuwa da jama’a kalubale ne da aka fuskanta a 2016. To sai dai sanar da kame  gandun dajin Sambisa daga hannun Kungiyar Jama’atu Ahlus Sunnah Li Dawatti Waljihad da musanta hakan da shugaban kungiyar ya yi muhiman batutuwa ne da suka faru a shekarar.

Symbolbild Afrika Markt Bunt (P. U. Ekpei/AFP/Getty Images)

‘Yan Najeriya ba za su mance da irin halin da tattalin arzikin kasar ya samu kansa a ciki ba, musamman matsin rayuwa, hauhawan farashin kaya da ma gazawar gwamnati na biyan albashi ga ma’aikata a wasu lokuta. A fanin siyasa kuwa rigingimun da ke faruwa a jamiyyar adawa ta PDP baya ga darewa gida biyu da ma kama hanyar rushewa, yayin da ita kanta APC ta ke zaki irin na ganga da ake tsoro me zai biyo baya saboda rikicin cikin gida.

Al’ummar Najeriyar dai na cike da fata na samun sauyi musamman a fanin tsaro da tattalin arziki saboda  karuwar farashin mai da ma yawan man da Najeriyar ke hakowa, a bangaren guda ga yadda alumma suka yi noma sosai duk da tsadar da kayan abincin ke yi a kasar.

You may also like