
Asalin hoton, OTHER
Jami’an tsaron da ke aiki na musamman na kulawa da iyakokin Najeriya da makwabtanta, domin hana satar shigar da kayan da gwamnati ta haramta, sun koka da rashin biyansu alawus-alawus na aikin.
Ma’aikatan sun koka ne tare da yin kira ga wadanda lamarin ya shafa a kan su taimaka a biya su hakkokinsu.
Daya daga cikin ma’aikatan da BBC ta tattauna da shi da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce, suna wahala kwarai da gaske a aikin.
Mutumin ya ce, ma’aikatan da ke aiki a iyakokin Najeriyar don sanya idanu da kuma hana shigar da kayan da aka haramta, sun hadar da sojoji da jami’an hukumar hana fasa kauri da na hukumar shige da fice da kuma na hukumar ‘yan sandan ciki wato DSS.
Ya ce, “ Muna wahala kwarai da gaske a wannan aiki da muke na shugaban kasa, don har yanzu ba a biya mu ba shekara daya da wata hudu ke nan.”
Jami’in ya ce, a lokacin da suka fara aikin lokacin Marigayi Abba Kyari da Hamidu Ali, shugaban hukumar hana fasa kauri, sun tsaya tsayin daka wajen ganin ana biyansu hakkokinsu a kowa ne wata.
Ya ce, ‘’ Duk da daina biyanmu alawus din da aka yi tsawon wadannan watanni ba mu daina aikin da aka sanya mu ba na ganin cewa ba a shigar da kayan da gwamnati ta haramta cikin Najeriya.”
Ya ce, “ Wasu sun mutu a cikinmu, an kashe wasu ba kuma abin da aka yi wa iyalinsu, gaskiya muna cikin wahala.”
Ma’aikacin ya ce, sun sha kai kokensu ga wadanda suka kamata babu abin da aka yi musu sai dai cewa za a yi a baki.
“ Abin takaicin ma, idan mutum ya fiye magana a kan batun hakkinsa sai a ce za a kore shi daga aiki.”
Ya ce, ”a gaskiya mun yi wa gwamnatin Buhari adalci, don haka mu ma ya kamata a yi mana adalci, saboda ba mu gaza ba wajen sauke nauyin da aka dora mana.”
“ Tsare kasar da muke yi, muna tare da sojojin Nijar da sauransu sai dai mu ga su ana biyansu amma mu ko oho sai tsabar wahala da muke sha,” in ji shi.
A don haka, “ Muna kira ga shugaban kasa da mai ba wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro da kuma shugaban hukumar hana fasa kauri, da su taimaka a ba mu hakkokinmu da muke bi tsawon watanni.
Saboda fargabarmu ita ce ga shi Shugaba Buhari ya kusa sauka, ba mu sani ba ko idan wanda ya hau zai biya mu ko a’a.”
Ma’aikacin ya ce, idan har gwamnatin ba ta gamsu da aikin da suke yi ba ne ya sa aka daina biyansu alawus, to ya kamata a sallame su daga aikin.