Najeriya Ba Ta Amince Da Rage Darajarta Da Kamfanin Moody’s Ya Yi Ba
WASHINGTON, D.C. – Kamfanin Moody’s ya rage darajar kasar mai arzikin man fetur a yammacin Afirka a makon da ya gabata zuwa Caa1 daga B3, yana mai cewa ana ganin tsarin kasafin kudi da bashi na gwamnati zai ci gaba da tabarbarewa, sanarwar da ta sa darajar alakar dala da kudin Najeriya ke tabarbarewa.

“Rage darajar Najeriya din da Moody’s ya yi, ya zo mana da mamaki domin mun gabatar da dukkan ayyukan da muke yi na tabbatar da tattalin arziki,” in ji minista, ga manema labarai a Abuja.

“Amma waɗannan hukumomi ne na waje waɗanda ba su da cikakkiyar fahimtar abubuwan da ke faruwa a cikin gida.”

Ta ce tana tsammanin awon S&P, wanda za a fitar ranar Juma’a, zai fi inganci.

“Awon S&P ba daidai yake da na Moody’s ba. Sun fito da ingantaccen tsarin kimanta awo,” in ji ta.

Najeriya dai ta fuskanci karancin man fetur sakamakon satar danyen mai a shekarun baya-bayan nan, duk da cewa man da ake hakowa ya fara karuwa kamar na da.

Haka kuma ta sha fama da karancin dala tare da yawan basussuka wanda ya ke lashe kudaden gwamnati.

Moody’s dai ya kawo waɗannan abubuwan ne a matsayin dalilan da suka kawo faduwar darajar.

-ReutersSource link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like