Najeriya Bata Da Kwarewar  Samar Da Yan Sandan Jihohi- Idris Babban Sifetan yan sandan kasarnan Ibrahim Idris,yayi kira ga masu kira da asamar da yan sandan jihohi da suyi duba kan kwarewar siyasar Najeriya.

Da yake magana lokacin da yake ganawa da gwamnoni jiya Alhamis a Abuja, Idris yace tsarin yan sandan tarayya shi yafi dacewa da kasarnan.

Yayi kira ga gwamnati da ta kara kason kudin da take bawa yan sanda ,kana yayi kira ga gwamnonin kan su goyi  bayan zartar da kudirin kafa asusun yan sanda dake gaban majalisar kasa. 

“Da zuciya daya  na yarda cewa tsarin yan sandan tarayya har yanzu shi yafi dacewa da kasarnan,idan har aka kara samar da kudi ga rundunar yan sanda  ina ganin za a kawo karshen aikata laifuka, ” Jimoh Moshood  mai magana da yawun rundunar ya jiyo shi yana fada. 

 “Wadanda suke hankoron ganin an samar da yan sandan jihohi yakamata su duba kwarewarmu a siyasa.”

Kan kudirin dokar yace ” Bari nayi amfani da wannan dama nayi kira ga masu girma gwamnoni kan su ja hankalin wakilansu a majalisar kasa kan su tabbatar an zartar da kudirin.

” Na tabbatar idan aka zartar da kudirin samar da asusun ya zama doka,za a samu duk wani kudi da ake bukata don samar da tsaro  cikin kasa.”

Yace hakan zai rage nauyin da jihohi suke dauka na tallafawa yan sanda da kayan aiki.

Da yake tabbatarwa da Idris goyon bayansu, Abdulaziz Yari,gwamnan jihar Zamfara yace harkar samar da tsaro abune   da ya shafi kowa. 

You may also like