Najeriya: An kama hanyar sake gina Arewa maso Gabas


 

 

Bayan share tsawon lokaci ana zaman jira gwamnatin Najeriya ta kaddamar da wani kwamitin da zai dauki alhakin sake ginin yankin Arewa maso Gabashin kasar da yakin boko ta haramun ya kassara.

Nigeria Schule Initiative Unicef Dalori Camp (picture-alliance/dpa/Unicef/Esiebo)

Karkashin jagorancin tsohon ministan tsaro na Tarrayar Najeriya Janar Theophilus Danjuma dai kwamitin mai wakilai daga kungiyoyi na fararen hula da dattawa daga yankin da ma wakilai na jihohi dai na da jan aikin sake ginin yankin da tsugunar da wadanda yakin ya raba da gidajensu cikin tsawon shekaru ukun da ke tafe.

Dubban miliyoyi na daloli ne dai ake da bukata wajen jan aikin da yake shirin kallon sake tsugunar da mutane miliyan biyu da dubu dari hudu sannan da sake ginin makarantu da ma ragowa na bukatu na rayuwar al’ummar yankin.

Ana dai sa ran kwamitin zai dauki dabarar kisan kudade na jihohi da na tarayya da ma wadanda ake saran samu daga kungiyoyin cikin gida da ma waje. A fadar shugaban kasar Muhammadu Buhari.

“Kwamitin ne zai zamo majalisar koli ta duk wani yunkuri na sake ginin yankin ko dai daga tarayya ko jihohi ko kuma kungiyoyin sa kai ciki da ma wajen Tarrayar ta Najeriya. Zai kasance a karkashi na gwamnatin tarayya sannan kuma mun dora masa alhaki na fitar da dabaru da kuma hanyoyin kaiwa ga sake ginin yankin na Arewa maso Gabas.”

Tsallen murna dai na zaman karatu na jihohin yankin da ke kallon kafa kwamitin a matsayin dama ta sabuwa ta rayuwa a tsakanin miliyoyin al’ummar yankin.

Nigeria Unruhen Islamisten Maiduguri Selbstmordattentäter (Imago)Rikicin Boko Haram dai ya daidaita Arewa maso Gabashin Najeriya

Senator Bindow Umar Jibrilla dai na zaman gwamnan jihar Adamawa kuma daya daga cikin jihohin da za su ci gajiyar shirin mai taken “Tsari na Buhari” da kuma ya ce ‘yan jiharsa na da bukatar sake gina hanyoyi da ma makarantun da aka kai ga lalatawa sakamakon ayyukan kungiyar Boko Haram.

To sai dai kuma ko ma wane tasiri kwamitin ke iya yi ga kokari na sake komawa bara a yankin dai, jeri na bukatu na da yawa a yayin kuma da kudaden ke zaman na kalilan na ayyukan kwamitin yanzu haka.

Naira miliyan dubu 23 ne dai ke cikin asusun kwamitin da ya samu alkawarin Naira miliyan dubu 50 tun daga farkon fari.

 

Senata Ali Ndume da ke zaman daya a cikin ‘yan kwamitin dai ya ce ceto ga rayuwar al’umma ne zai fara daukar hankalin kwamitin kamin kaiwa ga karkata zuwa ga gidaje.

Ko bayan jihohin yankin guda shida dai wata dokar majalisar tarayya ta kuma kara jihohin Kano da Filato da za su kai ga moriya cikin shirin na Buhari. Kuma a fadar gwamna na Kanon Abdullahi Umar Ganduje tuni jihar ta yi nisa a kokari na sake ginin al’ummar da suka ji babu dadi a wurin Boko Haram.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like