Najeriya na bincike kan zargin biyan miliyoyin kuɗi don yi wa ‘yan sanda ƙarin girma



Nigeria Police

Asalin hoton, Facebook/Nigeria Police Force

Hukumar kula da aikin ‘yan sanda a Najeriya ta ce ta kafa kwamitin bincike don bin diddigin zargin cewa ana biyan sama da naira miliyan bakwai kafin a yi wa manyan jami’an ‘yan sanda ƙarin girma.

Hukumar ta yi kira ga duk wani da ke da wata shaida kan wannan zargi, ya bayyana gaban ta, don gudanar da bincike.

Wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Ikechukwu Ani ya fitar ta ce matakan, martani ne kan wani rahoto da wata jaridar intanet a Najeriya ta buga mai taken ‘badaƙalar cin hanci ta tashi hankula a hukumar kula da aikin ‘yan sanda’.

Rahoton ya yi zargin cewa sai an biya cin hancin $10,000, kimanin naira miliyan bakwai, a yi wa manyan ‘yan sanda ƙarin girma a hukumar.



Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like