Najeriya na tattaunawa da Avengers


Shugaban Tarrayar Najeriya Muhammadu Buhari ya sanar da cewar gwamnatinsa ta soma tattaunwa da tsagerun NDA na Yankin Niger Delta .

A cikin wata sanarwa da ya bayyana shugaban ya ce gwamnatin tana tattaunawa da ‘yan Kungiyar Avengers na Yanki Niger Delta ta hanyar kamfanonin mai da ke a kudancin kasar.

Kungiyoyin tsagerun na Avengers sune ke da alhakin kai hare-hare a kan kamfanonin da ke yin aikin hako man fetir din a yankin Kudacin Najeriya a kan bukatunsu na ganin an yi adalci wajen raraba kudaden man da ake samu ga yanki, wanda ke fuskantar gurbatar muhali a sakamakon aikin na hakon man fetir.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like