Rundinar sojin Najeriya ta sanar da sake samun daya daga cikin ‘yan matan sakadaren Chibok da kungiyar boko haram ta sace yau sama da shekara biyu.
kakkin rundinar sojin kasar ne Sani Usman ya sanar da samun yarinyar a kauyen Pulka tare da cewa zai yi karin bayyani a nan gaba.
Pulka dai kauye ne dake kusa da garin Gwaza a jihar Borno sanan yana kusa da dutsen Mandara daya raba Najeriya da yankin arewa mai nisa na Kamaru.
Wannan dai na zuwa ne a kasa da wata guda da mayakan na boko haramn suka sako wasu ‘yan matan sun kimanin 21 bayan wata tattaunawa tsakanin gwamnatin kasar da mayakan a shiga tsakanin kungiyar agaji ta red cross da kuma gwamnatin Swiziland.
A ranar 14 ga watan Afrilu na shekara 2014 ne mayakan boko haram suka sace tare da yin garkuwa da ‘yan matan su 276.
kawo yanzu dai ‘yan matan 196 ne suka rage hannun ‘yan ta’addan na Boko haram koda yake gwamantin najeriya ta ce tana nan tana tattaunawa na ganin an kubutar da dukkan ‘yan matan.
kawo yanzu dai gamnatin kasar ta ce tana tattaunawa da kungiyar na ganin an saki wasu ‘yan matan 83.