Najeriya: Shekaru 50 bayan kifar da gwamnatin Ironsi


Ranar 29 ga watan Yuli na shekara ta 1966 na da matukar muhimmanci a game da barkewar yakin basasa a Najeriya.

Odumegwu Ojukwu jagoran Biafara a shekarar 1967 a tsakiya lokacin da yake jawabi

 

 

 

A wannan rana ta 29 ga watan Yuli na shekarar 1966, hafsoshin soja mafi yawansu Hausawa da Fulani daga Arewacin Najeriya suka aiwatar da juyin mulki na biyu wanda ya zama kamar dai daukar fansa ne kan na farko a watan Janairu, inda ya zo a sakamakon rashin gamsuwa da sojoji da mazauna yankin Gabashin Najeriya suka nuna ga rashin tsari ko iya tafiyar da mulki daga ‘yan Arewa da Yarabawa da suka mamaye mulkin na Najeriya a wancan lokaci. Wannan juyin mulki na biyu ya zama sanadiyyar tashin yakin basasa da ya haddasa asarar rayuka masu yawan gaske, musaman na ‘yan kabilar Igbo mazauna Arewaci da kuma wadanda yakin ya rutsa da su tsakanin shekara ta 1967 zuwa 1970.

Masanin tarihi Mike Gould da ya gudanar da bincike a game da yakin na Biafra a madadin cibiyar al’amuran nahiyar Afika a London, ya ce babu shakka juyin mulkin na biyu shi ya kawo tashin yakin basasa da Najeriya ta yi fama da shi saboda a bayan juyin mulkin, sai aka sami wani gibi na mulki da ya kawo har ‘yan kabilar Igbo aka rika yi masu kisan gilla.

Nigeria Premierminister Sir Abubakar Tafawa Balewa 1963Firaminista Abubakar Tafawa Balewa da juyin mulki na farko ya ritsa da shi

Yakubu Gowon wanda ya karbi mulki dan Arewa ya rasa karfin da zai iya dakatar da wannan kisa na kare dangi kan al’ummar Igbo. Odumegwu Ojukwu wanda shi ma soja ne kuma shugaban al’ummar Igbo ya bayyana fushinsa ga wannan yanayi, inda har ya ce idan har ba a dakatar da kashe al’ummarsa ba zai yi gaban kansa ya dauki matakin da ya ke ganin ya dace.

Tun kafin yakin ya tashi sai da aka yi kokarin sulhu musmman tsakanin Yakubu Gowon da Odumegwu Ojukwu a garin Aburi na Ghana. Karkashin yarjejeniyar da aka cimma, Najeriya za a kasa ta zuwa yankuna masu cin gashin kansu. Bayan da Gowon ya kasa samun goyon bayan ‘yan Arewa kan yarjejeniyar, Ojukwu shi ma ya yi watsi da ita. Nkwachukwu Orji, masanin al’amuran siyasa ya ce iyalinsa sun fito ne daga Arewacin Biafra, saboda haka ba su fuskanci bala’in da yakin ya haddasa ga mazauna yankin gaba dayansa ba.

Odumegwu Ojukwu Beerdigung Tshohon shugaban kasar Ghana Jerry John Rawlings a hagu da tshohon jakadan Najeriya a Faransa da Ralph Uwechue tsohon mashawarcin shugaban kasa Ben Obi a bikin binne Ojukwu

Ranar shida ga watan Yuli na shekarata 1967, sojojin Najeriya suka kwato yankin Gabashin Najeriya bayan da Ojukwu da mukarrabansa suka sanar da bai wa yankin mulkin kansa ranar 30 ga watan Mayu na shekara ta 1967, karkashin sunan Biafra. A bayan yakin an sami alkaluma da suka banbanta a game da yawan wadanda suka rasa rayukansu a kisan na Arewacin Najeriya.

Heinrich Bergstresser mai sharhi kan al’amuran Najeriya ya ce har yanzu yankin Gabashin Najeriya na nan da burinsa na kafa ‘yantacciyar kasar Biafra. A ganinsa, al’ummar Igbo suna daukar ‘yan Arewa a matsayin mutane ne masu daraja ta biyu ko daraja ta uku kuma su ne ke da karfi, kuma ya kamata su yi mulkin kasar ta Najeriya.

You may also like