Najeriya Shin Hukumar EFCC Nada Ikon Rike Kadarorin Mutumin dake Kan Kujerar Gwamna?


 

 

Hukumar EFCC ta saka wa asusun Gwamna Fayose na jihar Ekiti takunkumi saboda wai an gano wasu kudade sun shiga asusun daga Kanal Sambo Dasuki mai ba shugaba Jonathan shawara akan harkokin tsaro a gwamnatin da ta shude.

Sanin kowa ne cewa Kanal Sambo Dasuki mai ritaya yana fuskantar tuhuma akan badakalar kudin sayen makamai a gwamnatin Jonathan da ake zargin an karkata kudaden zuwa kan wasu abubuwa daban.

Binciken da ake yi shi ya kaiga hukumar EFCC ta sawa asusun Ayo Fayose takunkumi alhali kuwa yana gwamnan jihar Ekiti.

Gwamnoni da shugaban kasa suna da kariya wadda ta hana a tuhumesu akan kowane laifi har sai sun sauka daga mukamansu. Daidai ne EFCC ta saka wa asusun Gwamna Fayose takunkumi duk da yana rike da mukamin gwamna?

You may also like