Najeriya ta biya ‘yan wasa bashinsu


 

 

A ranar Laraba ne dai ‘yan wasan Falcons suka gabatar da zanga-zanga a gaban majalisar dokokin kasar inda suka sha alwashi na rike kofi da ma lambobin girma da suka samu.

Flash-Galerie Frauenfußball WM Nationalmannschaft Nigeria (picture alliance/Sven Simon)

Gwamnatin Najeriya ta saki kudi sama da Dala miliyan daya dan biyan alawus-alawus na tawagar ‘yan wasan kwallon kafa a kasar. Ofishin akanta janar na gwamnatin Najeriya ya ce kudin da aka fitar Dala miliyan daya da dubu dari biyu ne wadanda za a bayar ga ‘yan wasan Super Falcons saboda rawar da suka taka a gasar wasan kwallon kafa ta mata ta Afirka da aka buga a Kamaru, da ma kudin wasanni na kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles da suka buga wasan share fagen zuwa gasar kwallon kafa ta duniya a shekarar 2018 kamar yadda jami’ai suka bayyana.

A ranar Laraba ce dai ‘yan wasan Falcons suka gabatar da zanga-zanga a gaban majalisar dokokin kasar inda suka sha alwashi na rike kofi da ma lambobin girma da suka samu har sai gwamnatin kasar ta biya su alawus-alawus nasu.

You may also like