
Asalin hoton, OTHER
Najeriya ta fuskanci koma a baya a jadawalin kasashe mafi kwarewa a fagen kwallon kafa a duniya.
Kafin fitowar sabon jadawalin, Najeriya na matsayi na 32 a teburin FIFA, to amma yanzu ta koma na 35.
Maroko wadda ta yi rawar gani a gasar kofin duniya da aka kammala ba da jimawa ba a Qatar, ta koma na 11 a duniya.
Kazalika Maroko ta sauko da Senegal daga ta daya a teburin FIFA na mafi kwarewa a Afrika.
Kafin a fitar da sabon jadawalin, Maroko na zaune ne ta 22 a duniya, yanzu kuma ta dawo ta 11.
Atlas Lions sun kafa tarihin zuwa zagayen kusa da karshe na gasar kofin duniya, wani abu da wata kasa a Afrika ko ta Larabawa bata taba yi ba.
Tawagar Super Eagles ta fuskanci koma baya, tun bayan gaza doke Ghana a wasan share fage na zuwa gasar kofin duniya.
Kuma hakan ya hana ta zuwa gasar ta Qatar 2022 da aka kammala.
Brazil ce ke ci gaba da zama ta daya a teburin, sai Argentina da ta lashe kofin duniya ke binta.