Najeriya Ta Mayar Da Bakin Haure 18,Yan Kasar Nijar Zuwa Gida.


Hukumar kula da shige da fice ta Najeriya a jihar Neja ta mayar da wasu bakin haure 18,yan kasar Nijar zuwa gida. 

Kwanturolan hukumar a jihar, Tamuno  Oyedeji ta fadawa kamfanin dillancin labarai na kasa NAN, cewa an samu nasarar mayar da mutanen gida tare da taimakon  ma’aikatar mata da walwalar jama’a.

Tace hukumar da kuma ma’aikatar mata, sune suka samar da motocin da suka dauki bakin hauren zuwa garin Zangon Daura dake kan iyakar kasashen biyu a can jihar Katsina.

Takara da cewa an mika mutanen ga jami’an kula da shige da fice na jamhuriyar Nijar dake aiki a kan iyaka. 

Adedeji tace an mayar da bakin hauren ne zuwa gida saboda,basu da cikakkun  takardu.

 “kasancewarsu a jihar barazana ce ga tsaron al’ummar jihar “tace 

Oyedeji tace hukumar zata cigaba da daukar matakan kariyar tsaro, dan kare al’ummar jihar.

Ta kuma ce an kara jibge jami’an hukumar a garin Babana, dake kan iyaka domin maganin kwararowar bakin haure daga jamhuriyar Benin.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like