Najeriya Ta Sake Komawa Matsayi Na Daya A Afrika Kasashe Masu Yawan Fitar Da Man Fetur Bayan da ta shafe sama da watanni 8 a matsayi na biyu cikin jerin ‘kasashen da suka fi kowadanne fitar da yawan d’anyen man fetur a Nahiyar Africa, Nijeriya ta sake dawowa matsayi na daya. Kasar Angola ta sha gaban Nijeriya tun a watan Maris din 2016.
Wani rahoto da ‘kungiyar OPEC ta fitar na watan Disambar 2016 wanda ta nazarta ya nuna cewar Najeriya ta fitar da ganga miliyan 1.78 a kowacce rana inda ita kuma Angola take fitar da ganga miliyan 1.67 a kowacce ranar wannan wata.
Aiyukan tsagerun Niger-Delta na fashe-fashen bututun mai tun daga karshen shekarar 2015 har zuwa cikin shekarar 2016 sun taimaka kwarai wajen hana Najeriya cimma burinta na dinga fitar da ganga miliyan 2.2 a kowacce rana

You may also like