Nijeriya ta samu bashin dala biliya daya a cewar Bankin raya kasashen Afirka wato ADB. A yau ne aka amince a mika wa gwamnatin tarayya ta Nijeriya dala miliyan 600 a matsayin kason farko na bashin da shugaba Muhammadu Buhari ya nema.
A wata sanarwa da bankin ya fitar, ya bayyana cewa an bada umarnin baiwa Nijeriya dalar Amirka biliyan daya, don haka daga ciki a aka amince a mika dalal biliyan 600, cikin kason da kasar ta nema don fita cikin rikicin kudi da ta fada.
Shugaban bankin na ADB Akinwumi Adesina, ya ce a nan da watanni da ke tafe za’a sake bai wa Najeriya bashin Dala miliyan dari hudu, inda ya kara da cewa hakan zai taimaka don ceto Nijeriya daga gibin kasafin kudi da kuma matsalar tattalin arziki da ta fada ciki.
Rikicin ‘yan tawayen Niger Delta da yaki da Boko Haram da faduwar farshin mai, sai kuma uwa uba, berayen da ke cikingwamnatin Najeriya, sune musabbabin tsiyacewar kasar, da ke ta gaba a arzikin mai cikin nahiyar Afirka, amma yanzu ta ke yawo da kokon baran nemo basuka.