Najeriya Ta Samu Gagarumin Ci Gaba A Harkar Noma – Buhari


Shugaban Kasa, Muhammad Buhari ya bayyana cewa an samu gagarumin ci gaba a harkar noma ta yadda a halin yanzu mutane da dama musamman matasa suka shiga cikin harkar gadan gadan.

Shugaban ya yi wannan ikirarin ne a lokacin da ya karbi bakuncin Jakadan kasar Bangaladash, Manjo Janar Kazi Sharif Kaikoband a fadarsa da ke Abuja inda ya nuna cewa a halin yanzu Nijeriya ta rage shigowa da kayayyakin abinci daga waje a maimakon haka, tana kokarin ganin tana fitar da abinci da ta noma zuwa kasashen ketare.

You may also like