Najeriya Ta Sassauta Kudaden Wasu Kayayyaki Da Ake  Shigowa DasuNijeriya ta sassauta kudaden fito akan wasu kayayyaki da ake shigowa da su cikin kasar da ya kama daga kashi 20 zuwa 5 cikin dari. Gwamnatin ta ce ta dauki matakin ne domin bunkasa tattalin arzikinta.
Daga cikin kayayyakin da matakin ya shafa akwai ganyen shayi da madara da sarrafaffen tumatur da kuma magunguna. Sannan sassaucin ya shafi kayayyakin gini da kuma wadanda masaku ke amfani da su.
A karshen 2016 ne gwamnatin Nijeriya ta sanar da karin kudaden fiton akan kayayyakin kasaita da suka hada da motoci da sauransu.
Alhaji Ali Madugu mataimakin shugaban kungiyar masu masana’antu a Nijeriya, ya ce matakin na da muhimmanci duk da cewa akwai inda ya kamata a yi gyara.
A cewar Madugu wasu kayayyakin bai kamata a rage kudaden fitonsu ba musamman wadanda ake samarwa a Najeriya.
Gwamnatin Buhari dai na kokarin ganin an rage dogaro ne da kayayyakin da ake shigowa da su a cikin kasar wanda zai taimaka ga mayar da hankali ga wadanda ake samarwa a kasar.

You may also like