Gwamnatin Najeriya ta amince da sayan jiragen yaki masu saukar Ungulu daga kasar Rasha.
A watan Nuwamba mai zuwa hukumomin Rasha zasu mika jiragen yakin guda biyu ga Najeriyar, yayinda kuma a shekara ta 2017, Rashan zata karasa mika karin jiragen yakin guda goma.
A watan da ya gabata ne babban Hafsan Sojan saman Najeriya Air Marshal Sadiq Abubakar ya sanar da shirin sayo Karin jiragen yakin.
Sayan jiragen masu saukar Ungulu, zai taimakawa rundunar Sojin Najeriya magance tada kayar baya a yankin arewa maso gabashin kasar, da kuma yankin Niger Delta da ke kudancin kasar.