Najeriya Ta Siyo Jiragen Yaki Guda 14A yayin da Rundunar Sojin Nijeriya ke kokarin kawo karshen ta’addanci wajen murkushe kungiyar Boko Haram, Gwamnatin Nijeriya ta ce ta sayo jiragen yaki kimanin 14 don karfafa gwiwar rundunonin sojin wajen tunkarar kalubalen tsaro da Nijeriya ke fuskanta.


Gwamnatin ta kara bayyana cewa nan bada jimawa ba zata sayo karin wasu jiragen yakin daga Amurka domin taimaka wa dakarun sojin kasar wajen murkushe kungiyar Boko Haram inda tace zata tura ministan tsaron Nijeriya zuwa Amurka domin yi wa ‘yan majalisar dokokin Amurka bayani kan batun sayen jiragen yakin da kasar ke nema daga Amurkar.

Nijeriya dai ta shafe shekaru tana fafutikar sayo jiragen yakin daga Amurkar amma gwamnatin Barack Obama ta ki amince wa da bukatar saboda fargabar da ta nuna ta yiwuwar a yi amfani da su wajen keta hakkin bil’adama.

Sai dai ministan tsaron Najeriya Mansur Muhammad Dan-Ali, ya ce nan bada jima wa ba ne zai ziyarci Amurkar don tattauna batun sayen jiragen yakin da zarar ya samu amincewar shugaba Muhammadu Buhari game da ziyarar.

Gwamnatin Nijeriya ta sha cewa yakin da take yi da Boko Haram yana fuskantar cikas daga dokokin Amurka inda tun a watan Fabrairu ne Shugaba Trump da takwararsa Muhammadu Buhari suka tattauna batun sayar da makaman a wata tattaunawa ta waya da suka yi

You may also like