Najeriya ta yi asarar dala biliyan 7 saboda hare-haren tsagerun Niger Delta


 

Gwamnatin Najeriya ta ce, ta yi asarar kudi har dala biliyan 7 a cikin shekara 1 sakamakon hare-haren tsagerun Niger Delta kan bututai da kamfanunnukan man fetur da ke yankin kudu maso-kudu.

Shugaban Kamfanin mai na kasar NNPC Dakta Mai Kanti Baru ya shaidawa manema labarai a Abuja cewa, ta’addanci a yankin Niger Delta ya janyowa Najeriya asarar kudaden shiga.

Ya ce, ban da matsalolin tsaro, akwai matsalar siyasa da tattalin arziki da ma ta shari’a da ke shafar bangaren samar da man fetur a kasar.

Baru ya ce, a wannan shekarar ta 2016 an yi asarar gangar mai dubu 7 sakamakon hare-haren da ‘yan tawayen Niger Delta ke kai wa. Hakan na nuna cewa, kamfanin NNPC ya rasa kaso 60 cikin 100 na man da ya ke fitarwa a shekara.

You may also like