Najeriya za ta ci bashin makudan kudade daga bankin duniya | Labarai | DWJihohi da dama a kasar da ta fi yawan al’umma a nahiyar Afirka na fama da rashin isasun kudaden shiga, matakin da ke kai su ga cin bashi domin biyan albashi da ma gudanar da wasu muhimman ayyukan raya kasa.

Bankin duniya ya ce Najeriya ta taimaka matuka wajen rage wahalhalun yin kasuwanci ga ‘yan kasar, sai dai har yanzu an gaza yin nasarar shawo kan ‘yan kasuwar kasashen ketare don habaka hannayen jari idan aka kwatanta da wasu kasashe. 

Ko baya ga biyan albashi da ke zama makasudin ciwo wannan bashi, kazalika za kuma a yi amfani da kudaden wajen samar da ayyuka ta hanyar kuwanci da kuma inganta hanyoyin sadarwar kasar gami da kyautata cinikayya tsakanin ‘yan kasuwa da bangaren gwamnati.
 You may also like