Najeriya Za Ta Kashe Dala Biliyan 7.5 Kan Tallafin Man Fetur Zuwa Tsakiyar 2023 



WASHINGTON, D.C. – Najeriya, wacce ita ce kasar da ta fi karfin tattalin arziki a nahiyar Afirka, ta kashe naira tiriliyan 2.91 kan tallafin mai a tsakanin watan Janairu zuwa Satumbar 2022, a cewar kamfanin man kasar na NNPC.

Hedikwatar NNPC

Hedikwatar NNPC

Hukumomin Najeriya sun jima suna korafin cewa wadannan kudade hana kasar samun walwalar gudanar da wasu ayyuka a sauran ma’aikatu.

Shugaban Kasar Najeriya Muhammadu Buhari

Shugaban Kasar Najeriya Muhammadu Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya sanya hannu kan kasafin kudin shekarar 2023 na Naira tiriliyan 21.83 a ranar Talata, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 49, bayan da ‘yan majalisa suka kara kasafin kudin da kashi 6.4% tare da kara hasashen farashin man fetur.

-Reuters



Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like