Najeriya za ta kori wasu ‘yan kasar waje da aka kama yayin kai wa Boko Haram farmaki


 

 

 

Rundunar sojin Najeriya ta ce, za ta mikawa Hukumar Kula da Shige da Fice ta kasar wasu mutane 6 ‘yan kasar waje da ta kama a yayin kai wa Boko Haram farmaki domin fitar da su daga kasar.

Mutanen sun hada da ‘yan kasashen Kamaru, Chadi da Jamaika.

Kwamandan Runduna ta 7 ta Sojin kasar Birgediya Janar Victor Ezugwu ya sanarwa da manema labarai a ranar Lahadi a birnin Maiduguri cewa, mutanen na cikin wadanda aka kama a yayin farmakai a lokuta daban-daban a kasar kuma an gano ba su da alaka da kungiyar ta Boko Haram.

JanaralEzegwu ya kuma ce, bincike ya nuna mutanen sun shiga Najeriya ba bisa ka’ida ba.

Suna daga cikin mutane 348 da aka wanke su bayan bincike kan cewa ba su da alaka da Boko Haram wanda gwamnati ta saka a yayin bukukuwan cika shekaru 56 da samun ‘yancin kan kasar.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like