Najeriya: Zargin cin hanci a majalisa


 

Hon Abdulmumini Jibril wanda majalisar ta dakatar sakamakon tona asirinta ya sake bankado wani zargin cin hanci da rashawa a fanin kudadden gudanarwa na majalisar.

Nationalversammlung in Abuja, Nigeria (cc-by-sa/Shiraz Chakera)

A  wani sabon yanayi na tonon silili kan zahirin, Hon Abdulmumini Jibril wanda majalisar ta dakatar sakamakon tona asirinta, ya bankado wani zargin cin hanci da rashawa a fanin kudadden da majalisar ke kshewa wajen gudanar da harkokinta.

Wannan dai abin boye ne ya fito fili ga ‘yan Najeriya domin wannan ne karon farko da ‘yan kasar suka sami bayani  kan zahirin kudadden da yan majalisar ke kashewa domin gudanar da harkokin majalisar.

Dan majalisar wakilan Hon Abdulmumini Jibrin da ta kai ga dakatarwa bisa zargin cin hanci da rashawa da ya yi wa shugabanin majalisar ya sake bankdo wannan lamari, inda ya bayyana makudan kudadden da ya ce ana rub da ciki a kansu da sunan gudanar da harkokin majalisar. Tonon sililin dai ya haifar da nuna wa juna ‘yar yatsa musamman a tsakanin ‘yan majalisar da kuma shugabaninta.

A cewar  wani dan majalisar wakilan Ahmed Baba Kaita “bincike ne kawai zai iya rarrabe aya da tsakuwa kan zargin cin hanci da rashawa a tsakanin bangarori biyu”. ‘Yan Najeriya na sa ido su ga matakin da hukumomin yaki da cin hanci da rashawa a kasar za su dauka wanda zai tabbatar da sahihancin yakin da shugaban kasar ke yi da cin hanci da rashawa a Najeriya.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like