Najeriya Zata Fara Fitar Da Kwantenar Doya 20 Zuwa Kasashen  Duniya  a Kowane Wata 


Kwamitin kwararru kan shirin Najeriya na fitar da doya ƙasar waje yayi kiyasin   fitar da tan 480 dai-dai da kwantena 20 a kowanne wata a shekarar 2018.
Farfesa Simon Irtwange shugaban kwamitin ya fadawa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN haka a Abuja ranar Litinin, yace za a iya cimma haka idan akayi maganin dukkan matsalolin da masu fitar da doyar kasashen waje suka fuskanta a shekarar 2017.
Irtwange ya ce tuni ƙasar Amurika ta nemi da arika tura mata kwantena 5 a kowanne dai-dai da tan 120 na doya kenan.
“Idan komai ya tafi dai-dai, hukumomin ƙasar Amurika suna bukatar kwantena 5 kowane wata kuma duk kwantena ɗaya na cin tan 24 na doya.
“Muna kokarin harhada buƙatar da ƙasashe daban-daban suke da ita na doyar a karshe idan mun hada komai muna sa ran za mu rika fitar da kusan kwantena 20 na doyar a kowane wata.
“Muna da tsarin aiyukanmu kuma mun shirya abubuwa da dama da za muyi.

“Muna aiki da hukumomin gwamnati da abin ya shafa domin samar da goyon bayan da ake bukata kan shirin,”yace.

You may also like