Najeriya Zata Rufe Wasu Daga Cikin Ofisoshin Jakadancin Ta Sakamakon Matsin Tattalin Arziki



Gwamnatin Nijeriya ta ce za ta rufe wasu daga cikin ofisoshin Jakadancinta da ke kasashen duniya saboda rashin isassun kudaden da za a gudanar da su.
Ministan harkokin waje Geoffrey Onyeama shi ya sanar da haka ga manema labarai yayin daya ke bayyana nasarorin da ma’aikatar shi ta cimma a cikin shekaru biyu.
Ya ce rage adadin ofisoshin jakadancin na daya daga cikin manufofin shugaban kasa Buhari, duba da rashin kudaden da kasar ke fama dashi.
Sai dai bai bayyana sunayen kasashen da abin zai shafa ba, saboda a fadar sa, gwamnatin tarayya ba ta tabbatar da amincewar ta ba.
Ya ce sun mika rahoton bayanai akan ofisoshin jakadancin ga shugaban kasa Muhammadu Buhari kuma suna jira ne ya yi duba a kai kafin su dauki matakin gaba.
Yanzu haka dai kasar nada ofisoshin jakadanci a kasashen 119.

You may also like