Nan da Awa 24, Boko Haram za ta Fadi Inda ‘Yanmatan Chibok Su ke – Aisha Wakil


 

chibok-girls

 

 

Aisha Wakil, lauya a hukumar kare hakkin dan adam ta kasa kuma daya daga cikin mutane ukun da rundunar sojojin Nijeriya suka ce suna nema a kwanakin ta bayyana cewa kungiyar ta Boko Haram ta shirye ta sansanta da gwamnati.

Ta bayyana cewa akwai yiwuwar kungiyar za ta fito da babbar sanarwa akan ‘yan matan Chibok din nan da awa 24 masu zuwa a shafinta na Youtube. A fadarta “tun da na dawo daga wajen sojoji, ban barsu sun sha ruwa ba.”

Aisha ta ce, yanzu dai hakarta ta cimma ruwa domin kuwa ‘yan kungiyar ta Boko Haram sun yarda su tattauna da gwamnati domin a dawo da ‘yan matan na Chibok.

Wannan al’amari dai ya zo ne sati daya kacal bayan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce a shirye gwamnatinsa ta ke ta tattauna da shugabancin Boko Haram din na asali domin a saki ‘yan matan.

You may also like