
Asalin hoton, Getty Images
Trump ya ce za a ga balbalin bala’i idan aka tuhume shi da laifi
Donald Trump ya zama shugaban Amurka na farko a tarihi da za a tuhuma da aikata wani mugun laifi.
Za a tuhumi tsohon shugaban kasar ne a New York a bisa zargin bayar da wasu makudan kudade na toshiyar-baki, kafin zaben shugaban kasar na 2016, ga wata fitacciyar ‘yar fim din badala, domin hana ta magana kan zargin da ake masa na yin mu’amulla da ita.
Bayan rade-radi da aka shafe wata da watanni ana ta yi, yanzu dai ta tabbata za a tuhumi Donald Trump da aikata laifin.
Duk da cewa zuwa yanzu ba a fito fili an bayar da cikakken bayani game da tuhumar ba, amma dai tuhuma ce da ke da alaka da irin rawar da ya taka wajen biyan kudi ga matar – Stormy Daniels.
Kasancewar a yanzu tuhuma ta tabbata a kansa dole ne tsohon shugaban Amurkar ya je New York inda za a dauki hoton zanen yatsunsa da na fuska da kuma na kwayoyin halittarsa.
Daga nan zai gurfana a gaban alkali a kan tuhumar, inda daga nan kuma kila a bayar da belinsa.
Wani dan jarida Daniel Lippman ya gaya wa BBC cewa, mai yuwuwa kowa ne lokaci daga yanzu a kama Trump:
Ya ce, ”yadda abin yake ke nan. Ko da kai tsohon shugaban kasa ne, idan aka tuhume ka da aikata mugun laifi, dole ne ka shiga hannun hukumar tsaro.
”Shi ba barazana ba ne ga al’umma, kamar wani mai mugun laifi da ke da hadari. Ba wai kamar yanzu zai gudu wata kasa ba ne. Yanzu haka suna tattauna yadda zai mika kansa,” in ji dan jaridar.
A wata doguwar sanarwa da ya fitar ta mayar da martani kan batun, Mista Trump ya bayyana lamarin da cewa bi-ta-da-kullin siyasa ne kawai ake yi masa.
Kuma lauyoyinsa sun ce ba wani laifi da ya aikata, tare da lasar takobin yakar lamarin a kotu iya karfinsu.
Shi kuwa lauyan matar da ke tsakar wannan zargi, Stormy Daniel, ya ce hukuncin da aka yanke na shari’a kan lamarin ba abin murna ba ne, kuma ba wanda ya fi karfin doka.
Wannan shari’a ka iya kasancewa ta farko a kan tsohon shugaban kasar, inda za a tuhume shi da aikata wani babban laifi.
Amma kuma ba lalle tuhumar ta kasance ta karshe a kansa ba, abu ne da zai zama kamar an bude babi ko sa dan ba kan hakan.
Domin a yanzu haka akwai wasu manyan bincike-bincike da ake yi masa guda biyu, da suka danganci bore da kutsen da aka yi a ginin majalisun dokokin Amurkar, Capitol.
Da kuma yunkurin sauya sakamakon zaben shugaban kasar na 2020, kuma wadannan batutuwa har ma sun fi wannan na yanzu karfi sosai.
A makon da ya gabata Mista Trumpya yi barazanar cewa za a ga balbalin bala’i muddin aka tuhume shi da aikata mugun laifi.
Wanda a kan haka, tsohon mukaddashin shugaban ma’aikata a fadar gwamnatin Amurkar a lokacin Trump, Mick Mulvaney, ya gaya wa BBC cewa, idan har tsohon shugaban kasar ya nemi angiza magoya bayansa su tayar da zaune tsaye a kan tuhumar, to kuwa lalle ya debo ruwan dafa kansa.
Amma kuma ya ce, tuhumar za ta iya taimaka wa Trump, domin ‘yan Republican hatta wadanda ba sa kaunarsa, kamar shi kansa za su tausaya masa da cewa ana yi masa makarkashiya ne ta siyasa ta hanyar amfani da hukumomin gwamnati.